Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe manoma biyu a gonakinsu a yankin Yangtu a jihar Taraba.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a kudancin jihar da ke shiyyar Arewa maso Gabas.
Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ussa a majalisar dokokin Taraba, Habila Timothy, ya bayyana cewa manoman sun fito ne daga ƙauyen Kpambo.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa manoman sun je gonarsu da ke Kwambai, garin da ya haɗa iyaka da ƙaramar hukumar da kuma yankin Yangtu.

A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya ce har yanzu rahoton bai kai ga ofishin ƴan sanda ba.
Ya kuma ƙara ba da tabbacin cewa hukumar ta ɗauki matakai kuma an yi nisa a kokarin kakkabe yan bindiga gaba ɗaya daga jihar.