Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da bada tallafin Naira dubu goma duk wata ga kowane matashi mai yin bautar ƙasa a jihar

Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Talata a sansanin matasa masu yi wa kasa hidima da ke Damare a karamar hukumar Girei, lokacin bikin rantsar da matasan rukunin C na shekarar 2023, su 1340, da aka tura jihar.
Ya ce hakan ita ce manufar gwamnatinsa na yin alfarma da kyautatawa mutane, da nufin rage radadin da cire tallafin man fetur ga matasa.

Haka kuma gwamnan ya ba da tallafin man girki jarka goma, buhunan shinkafa 50, shanu 10 ga matasan.

Gwamna Fintiri, ya kuma taya matasan murnan kammala karatun da suka yi a makarantu daban-daban, wanda ya bayyana cewa zai taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai.
Da yake magana a bikin mai sa ido hukumar NYSC a jihar, Jingi Denis, ya bayyana zaman lafiya da cewa ya inganta a jihar, ya ce mafiya yawan matasan hukumar za ta turasu zuwa kananan hukumomin jihar domin yi wa ƙasa hidima.