Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa kan sake karbo bashin dala biliyan 8.69.

Har ila yau, Tinubu a cikin tsarin karbar bashin Gwamnatin Tarayya daga shekarar 2022 zuwa 2024 zai karbi bashin Yuro miliyan 100.

Tinubu ya ce Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka za su tallafa wa bashin da Naira biliyan 2.5.

Shugaban ya ce wannan bashin da za a karbo an yi duba ne ganin yadda zai taimakawa tattalin arziki da kuma ci gaban kasar baki daya.

Tinubu ya kara da cewa wannan karbar bashin ya zama dole ganin yadda bangarori da dama na kasar ke cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci Majalisar da ta yi gaggawar amincewa da ciyo bashin don bai wa gwamnati damar yi wa al’umma abin da ya dace.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: