Gwamnatin tarayya za ta tara naira miliyan 585 da za a biya a matsayin tarar wadanda ke daure a gidajen gyaran hali da ke fadin Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya shaida wannan a lokacin da aka saki wasu da ke daure.

A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta fito da wasu mutane daga gidajen gyaran hali da ke Kano bayan an biya tarar da kotu ta yanke musu.

Daraktan ma’aikatar cikin gida, Dr Anayo Romanus-Nzekwe wanda ya wakilci Minista Dr. Tunji-Ojo a wajen fito da ‘yan gidan kason a Kano.

Ministan ya ce mutane sama da 4, 000 ke garkame a gidajen gyaran hali saboda sun gagara biyan tara ko kudin da Alkali ya yanke masu.

Tunji-Ojo ya yi alkawari gwamnatin tarayya za ta biya kudin da ake bin mutanen da ke tsare, adadin tara da hakkokin wuyansu da ya zarce naira miliyan 500.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: