Jirgin yakin sojin sama a Najeriya ya fadi tare da fashewa a sansanin sojin sama da ke Port Harcourt a jihar Ribas.

Lamarin ya faru ne a yau Juma’a 1 ga watan Disamba a birnin Port Harcourt da ke jihar wanda ya yi sanadin tarwatsewar jirgin.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu ainihin dalilin da ya jawo faduwar jirgin ba.

Rahoton jaridar Punch ya tabbatar da cewa hatsarin jirgin sojin sama ya fadi ne da misalin karfe 7:50 na safe.

Wata majiya ta ce yana cikin daki ya ji karar fashewar jirgin da safiyar yau Juma’a a sansanin sojin saman da ke birnin Port Harcourt.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: