kwamitin majalisar dattawa, ya yi barazanar kai karar wasu kamfanonin mai da gas zuwa hukumar EFCC.

Manema labarai sun ruwaito cewa kwamitin majalisar zai yi karar kamfanoni idan aka same su da laifin karkatar da tallafin Naira biliyan 135 da CBN ya bada.

Shugaban kwamitin harkar gas a majalisar dattawa, Sanata Agom Jarigbe ya aika da wannan gargadi sa’ilin da su ka yi zama da kamfanonin.

Bankin CBN ya fito da wani tsari inda ya tallafawa manyan kamfanoni da aron kudi.

Sanatoci sun bukaci jin yadda aka yi amfani da bashin.

Sanatan na jihar Kuros Ribas ta Arewa ya ce shi da ‘yan kwamitinsa a majalisar dattawa sun lura ba ayi amfani da bashin kamar yadda aka bukata ba.

Da aka tattauna da wakiliyar ma’aikatar harkar man fetur, Tribune ta ce Oluremi Komolafe ta nuna ba ta san CBN ta bada aron wadannan kudi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: