Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar cewa zai rufe asusun bankin duk wadanda ba su da lambar BVN ko NIN.

CBN ya bayyana cewa daga watan Afrilun 2024, duk asusun bankin da ba a hada da lambar BVN ko NIN ba, za su daina aiki.

Babban bankin ya umarci duk masu asusun banki da na e-wallet da su tabbata sun hada su da NIN ko BVN dinsu kafin ranar 31 ga watan Janairu, 2024.

Sanarwar da CBN ya fitar dauke da sa hannun daraktan kudade da na tsare-tsare, Chibuzo Efobi da Haruna Mustapha, ta ce daga watan Afrilun 2024, za a haramta sanya kudi ko cirewa daga asusun banki marasa BVN ko NIN.

BVN shi ne lambar tantance masu ajiyar banki wanda CBN ya bullo da shi, kuma kowane mutum aka hade duk asusunsa na banki da BVN daya.

NIN kuma ita ce lambar shaidar dan kasa, wanda a watannin baya Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa kowa hade nasa da lambobin wayarsa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: