Duk da cewar gwamnatin tarayya ta sanar da ƙara albashin ma’aikatan ƙasar sai dai biyan ya gagara tun daga watan Satumban da ya gabata.

Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayyar Najeriya sun bayyanawa wakilin jaridar Punch cewar, gwamnatin ta biya naira 35,000 ne kaɗai a watan Satumba kuma daga wannan lokaci ba a sake biyansu ba.

Shugaban kula da tsarin albashi na kasa Ekpo Nta ya sanar a wata takarda cewa, za aa fara biyan mafi karancin albashi naira 35,000 ne daga watan Satumba.

Wani babban maaikaci a ma’aikatar kula da albashin, ya ce sun karɓi tsarin mafi karancin albashi naira 35,000 iya na watan Satumba ne kaɗai.

Idan ba a manta ba, kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki daban-daban domin ganin na kara albashin ma’aikatan, wanda gwamnatin ta alkawarta za ta yi.

Kungiyar ta ce wajibi ne a kara musu albashi, kasancewar gwamnatin ta cire tallafin man fetur wanda hakan ke sanya maaikatan cikin garari na tsadar raayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: