An samu hatsaniya a sansanin horas da matasa masu yi wa kasa hidima a birnin Abuja.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba 13 ga watan Disamba inda wani soja ya lakadawa wani dan bautar kasa duka.
Yayin dukan, sojan ya fasa wa matashin wayar salula da kuma agogon hannu mai tsada yayin da matasan su ka fito zanga-zanga don nema wa dan uwansu hakki.

An sami wani faifan bidiyo inda matasan su ka cika harabar daraktar sansanin don bin kadi.

Wani daga cikin masu karbar horaswar a sansanin da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana wa manema labarai yadda abin ya kasance.
A cewarsa an bukaci su shiga lacca, wasu sun tsaya a wurin siyar da abinci sai su ka ji ana ihu ashe sojoji ne su ke korar masu bautar kasa.
Majiyar ta kara da cewa an bukaci matashin ya bayyana abin da aka fasa masa inda hukumomi su ka yi alkawarin biyanshi duk abin da ya yi asara.