Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa wata gobara da ta kama da safiyar ranar Laraba ta ƙone ofisoshi 17 a sakateriyar karamar hukumar Gwale.

 

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.

 

Abdullahi ya bayyana cewa gobarar ta tashi a sakatariyar ƙaramar hukumar awannin farko na safiyar ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023.

 

Sannan ya ce wurin da aka yi amfani da shi a matsayin ofis mai tsawon ƙafa 300 x 200 da sauransu, wanda a jimulla ya kai ofisoshi 17, ya ƙone gaba ɗaya.

 

Haka nan kuma ya bayyana cewa wasu motoci uku da aka ajiye a sakatareyar wutar ta shafe su amma ba sosai ba.

 

Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar ya ambaci sunayen motocin da wutar ta taɓa, wanda suka haɗa da 406 Peugeot guda ɗaya, Bas guda ɗaya da motar bayar da daukin gaggawa.

 

Ya ce a halin yanzu hukumar ta fara bincike domin gano musabbabin abin da ya kawo tashin gobara a sakateriyar Gwale.

Leave a Reply

%d bloggers like this: