Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wata mata mai shekaru 75 a duniya da ke safarar miyagun kwayoyi a kasar.

Hukumar ta kama matar ne dauke da tabar wiwi da jarkokin kwayar kodin a tattare da ita.
Jami’an hukumar sun kama matar ne a unguwar Oshodi da ke Jihar Legas dauke da jarkoki cike da kodin a ciki.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya tabbatar da kama matar, inda ya ce matar ta bayyana musu cewa danta da ake nema ruwa a jallo ne ya kawo mata kwayoyin domin ta ringa sayarwa.

Sannan Femi ya ce Jami’an hukumar sun kuma sake kama wasu mutune biyu dauke da kwayoyi fiye da na miliyan daya a filin sauka da tashin jiragen sama na Jihar ta Legas.
Baya ga haka hukumar ta kuma kama wasu mutane daban-daban da ke wasu Jihohi da ke safarar miyagun kwayoyi a Kasar da kuma kwayoyi kala daban-daban a tare dasu a makon da muka yi bankwana da shi.
Hukumar ta ce bayan kammala bincike za a dauki matakin da ya dace akansu.