Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC reshen Jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da takwas suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a Jihar.

Kwamandan Hukumar Mista Anthony Uga ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce hadarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Lahadi.

Hukumar ta ce hadarin ya faru ne a tsakanin wasu motoci guda Biyu akan hanyar Idiroko zuwa Ota a daren na Lahadin.

Uga ya kara da cewa mutune Goma ne hadarin ya rutsa da su maza biyar, mata hudu da kuma karamar yarinya daya.

Kwamandan ya ce maza biyu ne suka rasa rayukansu yayin da sauran mutane Takwas suka jikkata, inda aka mika wadanda suka jikkatan zuwa babban Asibitin Idiroko da ke Jihar wadanda kuma suka mutu aka mikasu ga ‘yan uwansu.

Sannan Mista Uga yaja kunnen direbobi da su guji gudin wuce sa’a domin kaucewa afkuwar hadari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: