Babbar coci a Jihar Kaduna ta karrama Shahararran malamin addinin musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Gumi, tare da Fasto Yuhanna Buru, bisa gudummawar zaman Lafiya da suke bai’wa Jihar.

Shugaban Cocin Fasto Christopher Solomon ya bayyana cewa sun karrama mutane biyun ne bisa gudummawar da suke bai’wa al’ummar Jihar wajen ganin an samu tabbataccen zaman lafiya.

Solomon ya Kara da cewa mutane biyun na kokarin ganin, an samu zaman lafiya a tsakanin addinai da ke fadin Jihar.

Bayan karrama mutanen sun nuna jin daɗinsu, bisa karramarwar da cocin ta yi musu.

Sannan sun yi Kira ga mabiya addinin musulunci da na kirista,da su zauna lafiya da junan ba tare da nuna bambanci ba.

Daga karshe a jawabannasu sun yi addu’ar Neman zaman lafiya a fadin Jihar harma da kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: