Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya ayyana kujerun sanatan Yobe ta Gabas Ibrahim Geidam, da Sanatan Ebonyi ta kudu Dave Umahi a matsayin kujerun da babu kowa akan su.

Bayan murabus din mutanen biyun, majalisar ta nemi da hukumar zabe ta INEC ta shirya zaben cike gurbi don cike guraban kujerun biyu.


Geidam da Umahi sun yi murabus daga kan kujerunnasu ne bayan da shugaban Kasa Tinubu, ya nada su a matsayin ministoci.
Shugaban ya nada Ibrahim Geidam ne a matsayin ministan kula da harkokin ‘yan sanda, yayin da Umahi kuma ke rike da ministan ayyuka.
Sanatocin sun yi murabus daga Majalisar dattawa ne tun a watan August da ya gabata, bayan samun mukamin na minista.