Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan cike gurbi na wasu mazabun ‘yan majalisun Jihar Bauchi.

 

Kwamishinan zaben Jihar Muhammad Nura ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a yayin wata ganawa da yayi da kamfanin Dillancin labarai na Kasa NAN a Jihar.

 

Kwamishinan ya ce za a sake zabukan ne bayan da kotun sauraron kararrakin zabe a Jihar ta bayar da umarnin yin hakan.

 

A cewarsa za a gudanar da zabukan ne a ranar 3 ga watan Fabrairu mai kamawa.

 

Bugu da kari ya ce mazabu 42 ne kotun ta bayar da umarnin sake zabukan cike gurbin.

 

Kazalika ya kara da cewa a yayin zaben hukumar za ta dauki ma’aikatan wucin gadi da kuma gudanar da taron kwamitin tuntuba kan harkokin tsaro ICCES.

 

Daga karshe ya kuma bukaci kowanne bangare daga cikin ‘yan takara da su bai’wa hukumar hadin kai tare da bin dokokin da ta sanya musu domin gudanar da zabukan ba tare matsala ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: