Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta soki kasafin kudin Jihar Rivers na shekarar 2024 da muke ciki na naira biliyan 800.

A yayin yanke hukunci a yau Litinin Alkalin kotun mai shari’a James Omotoso, ya bayyana cewa kasafin da gwamnan Jihar Fubara ya gabatar a gaban mambobin majalisar Hudu da ke bangarensa gwamnan bai inganta ba.


Alkalin ya umarci da gwamnan ya sake kasafin a gaban zauren majalisar bisa jagorancin Martin Amaewhule, da ke bangaren tsohon gwamnan Jihar Nyesom Wike.
Mai shari’ar ya kuma bai’wa gwamnan umarnin biyan ‘yan majalisar kudaden da ya rike musu tare kuma da sauyawa wasu daga cikin mambobin guraren aiki inda ya ce gwamnan bashi da hurumin yin hakan.