Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dalilin ta na ware naira biliyan 125 a bangaren ilmi a Jihar.

 

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare Musa Sulaiman Shanono ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce gwamnatin Jihar ta bai’wa bangaren ilmin fifiko domin kara inganta shi.

 

Shanono ya ce gwamnatin ta Kano ta himmatu ne akan kara inganta bangaren ilimi, wanda hakan ya sanya aka warewa bangaren kaso mafi tsoka fiye da sauran bangarori.

 

Kwamishina ya bayyana cewa a kowacce shekara gwamnatin za ta ci gaba da karawa bangaren na ilmi wani kaso domin kara inganta shi.

 

Shanono ya kara da cewa za a raba kuɗaɗen ne a Ma’aikar ilmi mai zurfi, da kwalejin Rabi’u Musa Kwankwaso, da Jami’ar Aliko Dangote, Kwalejin Aminu Kano, Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da kuma Sa’adatu Rimi da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: