Hadakar jami’an tsaro a Jihar Kebbi sun kai hari wani sansanin ‘yan bindiga da ke Jihar a ranar Talata, inda suka yi nasarar kashe dan bindiga daya.

 

A yayin sumamen jami’an sun kubutar da mutane hudu da su ka yi garkuwa da su tare da kwato makamai.

 

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya da ke garin Kyaftin Yahya Ibrahim ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Yahya ya bayyana cewa jami’an sun kai sumamen ne a kauyen Sabon Garin a karamar hukumar Shanga ta Jihar.

 

Kazalika ya ce jami’an sun kwato bindiga kirar AK47 guda uku, harsasai 142 kayan soji guda biyu da kuma sauran wasu makaman.

 

Kaftin Yahya ya ce bayan ceto mutune hudu da su ka yi an mikasu ga ‘yan uwansu, inda kuma jami’an ke ci gaba da farautar ‘yan ta’addan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: