Wani Baturen ‘yan sanda ya ki amincewa da karɓar cin hancin naira miliyan daya da wani dan bindiga ya bashi bayan an kama shi a wani otal a jihar Kaduna.

 

Rahotanni sun bayyana cewa dan bindiga da aka kama ya bayar da cin hancin daga cikin kudin fansa da ‘yan sanda suka kwato daga hannunsa a wani otal da ke unguwar Tafa.

 

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Mansir Hassan, a ranar Alhamis, an kama mutumin ne a ranar 19 ga watan Janairu, 2024.

 

Hedikwatar sashen rundunar ta samu sahihin bayanai game da zaman wanda ake zargin a otal din st Easyway a yankin Tafa.

 

Ya bayyana cewa jami’ansu karkashin jagorancin Baturen yan sandan yankin Tafa, sun kai farmaki otal din, inda suka kama dan bindigar mai suna Bello Muhammad daga jihar Zamfara tare da kwato kudi naira 2,350,000, wadanda ake zargin na satar mutane ne.

 

Ya ce a lokacin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amince cewa shi mai garkuwa da mutane ne da ke gudanar da ayyukan sa a dajin Kagarko a Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: