Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Sanusi Lamido Sanusi ya goyi bayan mayar da wasu sassan babban bankin kasar daga Abuja zuwa Legas.

Ya ce abu ne da ya dace a yi, inda ya yi watsi da masu adawa da batun sauya shekar da cewa suna yin makauniyar siyasa.


Yan Najeriya da dama sun soki yunkurin gwamnati na mayar da wani bangare na bankin CBN daga Abuja zuwa Legas.
Wasu ‘yan siyasar arewa sun yi tir da matakin, inda suka yi gargadin cewa hakan zai haifar da illa a siyasance.
Sai dai sarki Sanusi, wanda shi ne Sarkin Kano na 14, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sauya shekar wani mataki ne mai ma’ana.
Ya ce shima ya yi niyyar daukar wannan matakin a sa’ilin da yake shugaban bankin, amma bai samu isasshen lokacin ganin hakan ta tabbata ba.
Tsohon gwamnan bankin ya shawarci CBN da kada ya yi kasa a guiwa saboda matsin lamba na siyasa, yana mai cewa dole ne bankin ya kara ƙaimi wajen tabbatar da wannan matakin.