Fitaccan Malamin addinin Musulunci Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya soki mutane da ke kushe ayyukan Hukumar Hisbah a Kano.

Shehin malamin ya ce ba dai-dai ba ne abin da mutane ke yadawa cewa ba sa hukunci kan masu kudi sai talakawa.


Rijiyar Lemo ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu yayin wani karatunsa da ya gabatar.
Rijiyar Lemo ya ce ba dai-dai ba ne a wurin wanda ya san shari’ar Allah inda ya ce ka yi iya abin da za ka iya bada doka ko umarni.
Ya ce duk abin da ya fi karfin mutum ba a kama shi da shi inda ya ce ita barna idan har za a iya rage ta a rage hakan ma nasara ce.
Ya kuma shawarci mutane da su guji kushe ayyukan hukumar inda ya ce addu’a ya kamata a yi musu don isowa kan manyan ayyuka.
Shehin ya kara da cewa bai kamata ana kushe ayyukansu ba tun da su na iya kokari ya kamata a yaba musu.
Ya ce yawan laifukan yanzu sun ƙaru idan aka kwatanta da baya, amma yanzu abin ya yi muni tun ana jin kunya har an bari wannan shi ne matsalar sabon Allah.