Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Legas ta yankewa wani Fosto mai suna Feyi Daniels hukuncin daurin rai da rai bisa zarginsa da laifin aikata fyade ga mabiyansa.

 

Alkalin kotun mai shari’a Rahman Oshodi ne ya yankewa Foston hukuncin a zaman da kotun na yau Juma’a ,bayan kammala sauraron korafe-korefan da aka gabatar mata akan Foston.

 

Kotun ta tsare foston ne tun a ranar 25 ga watan Mayun 2023 da ta gabata, bisa zarginsa da aikata lalata da ‘yar shekara 25 a gidansa da ke Jihar.

 

Sai dai bayan kammala karantawa Foston kunshin tuhume-tuhumen da ake yi masa ya musammata zargi.

 

Inda kuma bayan sauraron shari’ar Alkalin ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan ajiya da gyaran hali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: