Gwamnatin tarayya ta biya ma’aikatan albashin watan Janairu.

 

Gwamnatin Najeriya ta biya albashin bayan galabaita da ma’aikatan su ka na tsawon kwanaki 12.

 

A jiya Litinin ne dai mu ka baku labarin yadda ma’aikatan ke cikin wani hali na rashin ganin albashinsu.

 

Rahotanni da mu ka samu daga ma’aikatan a mataki daban-daban sun tabbatar da cewar sun fara samun albashinsu tun a daren jiya Litinin.

 

Ko a watan Disamba ma sai da aka ɗauki wasu lokuta kafin ma’aikatan su samu albashinsu na watan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: