Jami’an yan sanda na a babban birnin tarayya Abuja sun samu masarar kama wasu mutane bakwai da su ka kware wajen yin garkuwa da mutane.

Daga ciki akwai mata sannna sun kwato kuɗi naira miliyan Tara.


Kwamishinan ƴan sanda na Abuja ne ya yi holen waɗanda ake zargin yau Laraba, ya ce mutanen da aka kama da ma hukumar na nemansu ruwa a jallo.
Waɗanda aka kama sun fito ne daga jihohin Kaduna, Naija, Katsina Borno Filato da babban birnin tarayya Abuja.
Kwamishinan y ace waɗanda aka kama sun amsa laifukansu sannan su na ba su haɗin kai sajen samun bayanan sirri.
Haka kuma jami’an sun kama wasu mutane 79 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
Daga ƙarshe ya ce za su gurfanar da mutanen a gaban kotu bayan sun kammala bincike a kansu.