Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya tsaf wajen daidaita farashin kayan abinci tare da daƙile hauhawar farashinsa.

Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana haka yayin da ya halarci taron sauyin yanayi da hauhawar farashi ranar Talata.


Ya ce gwamnatin na yin duk mai yuwuwa wajen daƙile hauhawar farashi da kuma sauyin yanayi.
Ya ce akwai shirye-shirye da su ka yi wajen wadata ƙasar da abinci da kuma ruwan sha.
Daga cikin tsarin daa su ka samar akwai raba taki da iri ga manoma da magidanta tare da kafa hukumar samar da abincita ƙasa.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da sa ido tare da bibiya a kan farashin kayan abinci a ƙasar.
Haka kuma gwamnatin za ta samar da tsarin da za a kare manoma da kuma gonakin da za a noma.
Sannan ya ce matakan da su ka ɗauka za su yi aiki tare da samar da sauyi mai ma’ana.