Hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta samu nasarar kama wasu matasa bakwai bisa zargin damfara ta yanar gizo.

 

An kama matasan a Makurdi babban birnin jihar Benue ranar Laraba.

 

Hukumar ta ce akwai wasu da take zargi sun buɗe cibiya domin bayar da horon yadda ake damfara ta yanar gizo.

 

Jami’an sun kama matasa uku da farko a wani gida da take zargi wajen ne da su ke horarwa a kan damfarar yanar gizo.

 

Daga cikin kayan da aka saamu a wajensu aakwai na’ura mai ƙwaƙwalwa ta taafi da gidanka wato laptop, katunan cirar kuɗi na banki, wayoyin hannu, janareta da mota kirar toyota corolla.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: