Majalisar wakilai ta tarayya a Najeriya ta roki shugaba Bola Ahmad Tinubu da ya rage kuɗin aikin hajjin bana wanda aka ayyana naira miliyan biyar.

 

A zaman majalisar da ya gudana yau Alhamis, ɗan majalisar mai wakiltar Maƙarfi da Kudan a jihar Kaduna Umar Ajilo ne ya gabatar da ƙudirin .

 

Ɗan majalisar ya miƙa ƙudirin ne bisa yadda ake zuwa aikin hajjin ke cikin shikashikan musulunci.

 

Majalisar ta fahimci cewar kuɗin da aka saka naira miliyan biyan matsakaita da ƙananan ba za su samu damar sauke faralin ba.

 

Duba ga halin da ake ciki majalisar ta nemi shugaban ƙasa da ya sake dubawa tare da yin wani abu na ragi daga cikin kuɗin da aka saka.

 

Idan ba ku manta ba a jiya, mun kawo muku labari cewar fiye da kashi 70 na maniyyata a jihar Jigawa sun kammala biyan kuɗin aikin hajjinsu kamar yadda hukumar ta bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: