Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwa don amincewa jihohin ƙasar kafa ƴan sanda a wani salo na magance matsalar tsaro.

 

Shugaban ya nuna amincewar tasa ne yayin da ya yi wani zama da gwamnonin ƙasar yau Laraba.

 

Shugaba Tinubu ya kira taron gaggawar ne a fadarsa domin tattauna hanyoyin da za a bi don kawo ƙarshen matsalar tsaro.

 

Zaman ya mayar da hankali a kan batun tsaro da tsadar kayan abinci, wanda jihohin su ka yi amanna cewar ƙasar ba ta da buƙatar shigo da abinci don sauke farashin na cikin gida.

 

Ministan yaɗa labarai a Najeriya ya shaida cewar ko da an cimma matsaya a kan haka, akwai ayyukan da za a yi wanda tattaunawa tsakanin jihohi da shugaban ƙasa zai tabbatar.

 

Tun a shekarun baya wasu daga cikin jihohin ƙasar ke neman amincewar gwamnatin tarayya domin kafa ƴan sandan jihohi wanda hakan zai bayar da damar saukaka ayyukan ta’addanci da ya addabi kasar.

 

Tuni wasu jihohi kamar Zamfara, Katsina Sokoto da wasu daga kusancin ƙasar su ka samar da ƴan sa kai tare da basu horo domin taimakawa tsaro a jihohin.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: