Ƴan bindiga a jihar Zamfara sun ɗauki sabon salo wanda ya tilastawa mutanen wasu ƙauyuka yin hijira.

Salon da ƴan bindigan ke yi na yi wa matan aure da ƴan mata fyade a cikin gidajensu, ya sanya da yawan mutane yin kaura daga kauyukansu.


A wata tattaunawa da BBC ta yi da wani magidanci, ya ce sun kashe mutane a Kalgon Kunchi da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar.
Ya ƙara da cewa kashi 70 na mutanen ƙauyen sun yi kaura zuwa wasu ƙauyukan.
Kafin haka, ƴan bindigan na shiga ƙauyen tare da yin awon gaba daa dabbobinsu, da kuma yin garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, sai dai a yanzu sun sauya salo.
Ya ce a yanzu su na zuwa tun safe su wuni a garin su na aikata fyade ga matan aure da ƴan mata a a kauyen.
A ɓangaren gwamnatin jihar, Sulaiman Bala Idris mai magana da yawun gwamnan ya ce gwamnatin na iya ƙoƙari don kawo ƙarshen lamarin a ƙauyen da ma sauran abubuwan da ke faruwa na ta’addanci a faɗin jihar baki ɗaya.