Ƙungiyar kwadago a Najeriya NLC ta ayyana fita zanga-zangar lumana ta kwanaki biyu bisa tsadar rayuwa a Najeriya.

 

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Joe Ajaero ne ya bayar da umarnin bayan wani zaman gaggawa daa kungiyar ta kira a yau a Abuja.

 

Sannan ƙungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin cika alkawuran da ta ɗaukar musu tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

 

Shugaban ya ce abin kungiya ne ganin halin da ƴan ƙasar ke ciki amma gwamnati ta yi watsi da halin da ma’aikata ke ciki na walwalarsu.

 

Ƙungiyar za ta yi zanga-zangar ne a ranakun 27/28 ga watan Fabrairu daa mu ke ciki.

 

Idan ba a manta ba, gwamnatin ta rarrashi ƙungiyar har ta amince da ci gaba da biyan naira 35,000 mafi ƙarancin albashi, ko da dai ƙungiyar ta nemi a biya naira miliyan guda matsayin mafi karancin albashi a ƙasar.

 

Haka kuma ƙungiyar dalibai ma a Najeriya ta yi kira ga ƙungiyar kwadago da kada su tafi yajin aikin domin halin da dalibai ke ciki da kuma matsalar tsaro.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: