Darajar naira na ci gaba da faduwa ƙasa warwas yayin da ake sauya dala guda a kan naira 1,845 a kasuwar bayan fage.

Matashiya TV ta gano yadda darajar naira ke ci gaba da faduwa yayin da ake ci gaba da karyar da ita a hukumance.
Faduwar naira na daga cikin dalilan da ke ƙara ta’azzara hauhawar kayan masarufi a Najeriya, musamman a wannan lokaci da mutane ke fama da tsadar rayuwa.

Ko a jiya sai da matasa su ka yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihar Oyo.

Masu motocin dakon mai ma sun bayyana yadda su ke asara, dalili ke nan da ya sa su ja jingine ayyukansu tun a jiya Litinin.
Har yanzu dai gwaamnatin Najeriya ta kasa shawo kan matsalar, ko da yake ta ce wahalar da kae sha wani lokaci ne kuma mutane za su dara nan da lokaci kankani.