Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya kwastam na shirin fara raba kayan abinci da ta kwace ga ƴan Najeriya don rage radadin halin yunwa da ake ciki

Kafin raba kayan abincin, sai hukumar ta tabbatar da inganci da kuma yiwuwar mutane su amfaneshi ta hanyar ci ko sha.


Shugaban hukumar na ƙasa Bashir Adewale ne ya bayyana haka yau a Abuja, ya ce su na kan shirye-shirye don ganin sun raba kayan abincin da sy ka kwace waɗanda aka shigo da su ba bisa ka’ida ba.
A wata sanarwar da Abdullahi Maiwada jami’in hulda da jama’a na hukumar ta ƙasa ya fitar yau, sanarwar ta ce tsarin da za su yi na daga cikin shirin shugaba Bola Tinubu dangane da harkokin abinci.
A halin yanzu hukumar na kna tsare-tsaren yadda za su raba kayan abincin ga jama’a don ganin an samar da sauƙi ga tsadar kayan abinci.
Idan ba a manta ba, ko a jiyaa matasa a jihar Oyo sai da su ka gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da hauhawar kayan masarufi.