Rundunar sojin saman Najeriya reshen jihar Kano ta samu nasarra kama wani rikakken mai garkuwa da mutane .

An kama Abdul Isah a garin Durbunde da ke ƙaramar hukumar Takai a Kano.


Mai magana da yawun rundunar ta ƙasa Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya tabbatar da haka wanda ya ce sun kamashi ne a yammacin jiya Litinin.
Ya kara da cewa sun kamashi ne bayan samun bayanan sirri a dangane da mabiyarsu shi da yaransa.
Wanda aka kama ana zarginsa da yin garkuwa da mutane a yankunan.
Daga cikin mutanen da ake zargin ya yi garkuwa da su har da wani Yakubu Ibrahim Tagaho wanda aka fi sani da Sarki n Noman Gaya.
Sun yi garkuwa da shi ne a ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar da ta gabata a gidansa da ke Takai.
A halin yanzu wanda aka kama na tsare hannun jami’an sojin kuma ana ci gaba da bincike a kansa.