Majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya za ta yi bincike a kan hare-haren da aka kai a jihar Zamfara.

 

Matakin ya biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa Hassan Shinkafi na jam’iyyar APC a zaman majalisar na yau Talata.

 

Majalisar za ta yi binciken a kan hare-haren da aka kai ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar wanda ya yi silar rasa rayuka da dukiyoyi masu yawa.

 

Hassan Shinkafi ya ce wajibi ne a binciki hare-haren musamman ganin yadda mutane ke cikin wahala ta tsadar rayuwa.

 

Ya ce hakan ya haifar da ƙarin damuwa musamman ga mutanen da aka kai musu harin ga kuma halin rayuwa da su ke ciki.

 

Majalisar ta buƙaci babban sufeton ƴan sanda na ƙasa da ya kafa wani kwamiti da zai yi bincike a kai tare da miƙa musu rahoto a kai.

 

Sannan majalisar ta buƙaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA da ta kai ɗauki tare da bayar da tallafi ga mutanen da lamarin ya shafa.

 

Sannan a sake aike da ƙarin jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

 

Idan ba ku manta ba, mun baku labari cewar yan bindiga sun kai hare-hare a jihar Zamfara ciki har da helkwatartar yan sanda ta ƙaramar hukuma.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: