Hukumar hana cin hanci da rashawa ta Najeriya ta kama wasu manyan ƴan kasuwar chanji ta Wapa a Kano.

A safiyar yau hukumar ta yi tsinke a kasuwar tare da kama wasu daga ciki.

Hakan ba ya rasa nasaba da ƙarin farashin dala da ake ci gaba da samu a kowacce rana wanda a yau ake sauyar da dala guda kan naira 1,900.

A labarin da mu ka kawo muku a asubahin wannan rana kun ji cewa gwamnatin za ta fitar da dala biliyan goma da nufin daaga darajar naira a ƙasar.

Ko a jiya ana sauya dala guda a kan naira 1845 a kasuwar chanji.

Shugaban kasuwar Alhaji Sani Dada ya tabbatar da kama mutane wanda ya ce jami’an sun tafi da su don gudanar da bincike.

Wani a cikin kasuwar ya shaidawa Matashiya TV cewar an tafi da wasu daga cikin ƴan kasuwar yayin da jami’an su ka shiga a safiyar yau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: