Majalisar dattawan Najeriya ta roƙi gwamnatin tarayya da ta dakata daga batun cire tallafin wutar lantarki.

Gwamnatin na shirin cire tallafin wanda ta fito ƙarara ta bayyana cewar ba za ta iya ci gaba da biya ba.

Idan za a iya tunawa shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur tun a jawabinsa na rantsuwa.

A zaman da majalisar ta yi a yau Laraba, ta roƙi gwamnatin daa ta dakata daga batun cire tallafin wutar lantarkin.

Rokon na zuwa ne bayan da ɗan majalisa Aminu Iya Abbas daga Adamawa ya gabatar da ƙudirin a zaman majalisar na yau.

Majalisar ta ce duba ga halin matsi da ake ciki bai kyautu a cire tallafin ba a wannan lokaci.

Ƙudirin ya samu goyon bayan mafi rinjaye a majalisar wanda ya sa aka yi kiran ga gwamnatin tarayya.

A makon jiya, ministan makamashi Adebayo Adelabu ya bayyana matsayar gwamnatin kan cewar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin lantarki ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: