Rundunar ƴan sanda a jihar Zamfara ta lashi takobin kawo ƙarshen dukkan ayyukan ta’addanci a jihar cikin watanni uku.

 

Kwamishinan yan sanda a jihar Yusuf Kolo ne ya yi alwashin yau yayin ganawa da ƙungiyar kwadago ta ƙasa reshen jihar, da shugabannin addinai, ƙungiyoyin masu zaman kansu da ƴan jarida.

 

Yusuf Kolo ya yi kira ga ƙungiyar kwadago da su janye daga fita zanga-zanga da su ka shiya yi a nako mai zuwa.

 

Kwamishinan ya ce gwamnatin tarayya da ta jihohi na shiri don ganin ta kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya.

 

Sannan ya basu haƙuri don ganin an baiwa gwamnatin dama, ya ce abinda gwamnatin ta fi buƙata a yanzu bai wuce addu’a ba.

 

Kungiyoyin sun ɗauki damarar yin zanga-zangar ne ganin yadda gwamnati ta ki cika musu buƙatunsu tun bayan cire tallafin man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: