Mahukunta a kasuwar chanjin kuɗi ta Wapa a Kano sun bayan da umarnin rufewa ba tare da bata lokaci ba.

Ƴan kasuwa sun yi cirko-cirko yayin da shaguna su ka kasance a rufe yau Alhamis.


Matashiya TV ta tuntuɓi shugaban kasuwar Alhaji Sani Dada wanda ya ce sun ɗauki matakin haka ne domin bibiya a kan kamun kazar kuku da jami’an tsaro ke yi wa ƴan kasuwar.
Idan za a iya tunawa a jiya Laraba jamian tsarin EFCC da ƴan sanda sun shiga kasuwar tare da kama mutane masu yawa.
Shugaban ya ce mutanen da ke sana’ar su na da lasisinsu, a don haka su ka rufe har sai sun bibiya a kan kamun da ake yi musu.
A jiya ana sauyar da dalar Amurka guda kan naira 1,900 zuwa 1,940 wanda hakan ke ƙara sa fargaba ga ƴan Najeriya.
A wata zantawa da mu ka yi da shi a baya ya shaida cewar, ko gwamnati ta shafe fiye da shekaru uku ba ta bayar da dala ga ƴan kasuwa da masu son fita ƙasashen ƙetare.
Hauhawar dala dai ya haifar da tsadar kayayyaki a Najeriya wanda ake ci gaba da fuskanta a halin yanzu.