Gwamnatin jihar Benue ta bai wa makiyaya wa’adin kwanaki 14 da su fice daga jihar.

 

Gwamnan jihar Hyacinth Alia ne ya bayyana haka yayin wani zama da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a jihar.

 

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Sir Tersoo Kula ya bayyanawa manema labarai cewar, gwamnatin ta kafa kwamitin mutane bakwai don tabbatar daa dokar wanda su ka fara aikinsu a jiya Laraba.

 

Dokar za ta shafi makiyaya da ke karya doka tare da haifar da fitina a jihar.

 

Gwamnatin ta ce dokar da aka kafa a kan kiwo ta shekarar 2017 ta na nan kuma har yanzu ta na aiki.

 

Sannan ya yi kira ga mutanen jihar da au kwantar da hankalinsu don ganin komai ya daidaita.

 

A gefe guda kuma ya buƙaci jama’a da shugabannin gargajiya da su kai rahoton duk wani makiyayi da ya ketara doka a jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: