Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi umarni ga hukumar ƙidaya a ƙasar da ta gabatar da bayanan shirinta na ƙidaya da aka dakatar.

Kotun mai zama a Abuja a yau Alhamis ta umarci hukumar da ta gabatar da bayanan cikin kwanaki Bakwai.


Kotun ta buƙaci a gabatar mata da bayanan yadda za a kashe kuɗaɗen a aikin ƙidaya da za su yi.
A baya an shirya gabatar da aikin a shekarar 2022 aka daga zuwa shekarar 2023.
Gab da karewar wa’adin shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da aikin ƙidayar.
A halin yanzu hukumar ta tsayar da watan Nuwamba na shekarar da mu ke ciki domin yin ƙidaya a Najeriya.
A watan Yuni na shekarar 2023 hukumar ta ce za ta kashe naira biliyan 200 don yin aikin ƙidaya a Najeriya.
A sakamakon haka wani lauya a Abuja ya gurfanar da hukumar a gaban kotu domin gabatar da bayanan yadda za ta kashe kudin a yayin aikin.