Rundunar sojin Najeriya ta hallaka rikakken dan bindiga da ya jagoranci garkuwa da ɗaliban Yauri, Greenfield, da harin da aka kai makarantar horas da sojoji.

Jami’an na runduna ta ɗaya da ke Kaduna su ka kashe Boderi a jiya Laraba tare da wani ɗan bindiga Bodejo.


Jami’an sun kashe ƴan bindigan ne a wani hari da su ka kai musu na kwanton bauna.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Onyema Nwachukwu ya fitar yau.
Ya ce sun hallakasu ne a yankin Bada-Riyawa da ke kan titin zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Haka kuma akwai wasu ƴan bindiga shida da aka kashe yayin da sojin su ka kwato jindigu kirar AK47 guda biyu, da harsashi mai yawa tare da lalata babura guda 19.
A harin da su ka kai na musamman a ƙananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi sun samu nasarar kwato makamai masu yawa daga wajen yan bindigan.
Sabon shirin sojin da su ke yi na daga cikin manufarsu ta kawar da dukkanin ƴan bindiga da su ka addabi yankunan.