Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta fitar da rahoto a kan zaɓen da ta gabatar na shekarar 2023.

 

A wata sanarwa da kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma shugaban wayar da kan jama’a kan katin zaɓe Sam Olumekun ya sanyawa hannu.

 

Ya ce tabbatar da aikin na’urar BVAS ya sa su ka yi aiki da ita a babban zaɓen da ya gabata.

 

Daga cikin sabbin dabaru da fasahar sadarwa da su ka yi amfani da ita, sun yi ne bayan samun darasi daga zabukan baya da kuma annobar korona.

 

Zaban 2023 shi ne zaɓe na farko da aka gabatar tun bayan kwaskwarima da aka yi wa dokar zaɓe a Najeriya.

 

Hukumar ta ce ta fuskanci ƙalubale mai yawa wajen saka sakamakon zaɓe daga rumfar zaɓe kai tsaye a shafin da aka ware na yanar gizo.

 

Hukumar ta ce zaɓen da aka yi da ya gabata zaɓe ne sahihi kuma wanda aka yi ba tare daa hargitsi ba.

 

Sanna ta tabbatar da cewar sakamakon da ta saka a shafinta da ta ware don saka sakamakon zaɓe bayan zaɓen shugaban kasa da ƴan majalisar wakilai da majalisar dattawa ingantacce ne.

 

Kuma rashin saka sakamakon zaɓe da aka yi daga rumfunan zaɓe an samu ne sanadin tangardar sadarwa da aka fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: