Hoton man feturMan Fetu

Hukumar ƙididdiga a Najeriya NBS ta ce an samu raguwar shigo da tataccen man fetur tun bayan cire tallafinsa.

 

Ministan yaɗa labarai da wayar da kai a Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi dangane da nasarorin gwamnati wanda ta samu cikin watanni tara.

 

A bayaninsa wanda ya fitar a yau, ya ce shugaba Tinubu ya yi alƙawura yayin rantsuwa fara aikinsa.

 

Daga ciki akwai cire tallafin man fetur wanda ya ce gwamnatin ba za ta iya ci gab ada biya ba, sai kuma karkatar da kuɗaɗen zuwa ayyukan da za su amfani jama’a kamar ilimi, lafiya, da sauran ayyuka.

 

Ya ce tun bayan ayyana cire tallafin man fetur, an samu raguwar shigo da shi da kashi hamsin %50 a Najeriya.

 

Sannan an samu ƙarin hako danyen mai a ƙarshen shekarar 2023 da ta gabata.

 

Sannan gwamnatin na samun bayanai a kan rarar da ake samu a sakamakon cire tallafin wanda za a yi amfani da su don yi wa jama’a ayyuka.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: