Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce duk da ƙalubale da suka da yake samu ba zai sauya masa ra’ayi a kan manufofinsa ba.

Shugaban ya bayyana haka ne jiya Alhamis yayin da ya tarbi ƙungiyar kasuwanci ta CCA a fafarsa.


Ya ce manufar da ya sa a gaba na sauya fasalin tattalin arziki ba zai sauka aa kai ba duk da kalubalen sa yake fuskanta.
Ya ce bunƙasa tattalin arziki shi zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Cire tallafin man fetur na daga cikin alkawuran da ya yi tun kafin zaɓe kuma ya jaddada bayan an rantsar da shi.
Ana fuskantar tsadar rayuwa da ba a taɓa samu ba a Najeriya, wanda hakan ya sanya aka yi zanga-zanga saboda yunwa da ake fama a kasar.
Sai dai shugaban ya ce duk da halin ƙasar ke ciki, ba zai sauya masa ra’ayi na ganin ya sauya fasalin tattalin arziki ba.
Tun tuni sarakunan gargajiya da shuwagabannin addinai ke kira daa a kawo hanyar da za a samu sassauci, don gudun wani abu mara daɗi ya auku sakamakon matsi da talakawa su ka shiga.