Alamu na nuni da cewar ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashe yammacin Afirka wato ECOWAS na shirin dage taakunkumin da ta sakawa ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.

Rahotanni dun nuna cewar za a cire takunkumin da aka sakawa ƙasashen bayan daa su ka bayyana ficewa daga cikin kungiyar.


Idan za a iya tunawa a ranar 15 ga watan Fabrairu daa mu ke ciki, ƙasashen su ka nuna aniyar kafa sabuwar kungiya da ka iya zama kishiya ga ECOWAS.
An samu musayar yawu bayna da soji su ka karɓe ikon mulkin ƙasar Nijar wanda a lokacin ne lamarin ya dada zafafa.
Idan za a iya tunawa shugaba Bola Tinubu ya bukaci ƙasashen da su bayar da dama domin sake zama a teburin sulhu, domin su a shirye su ke da hakan.
Ya ce bai kamata a datse alakar da ta daɗe da wanzuwa ba, duk da cewar akwai al’adu da harshe da ƴan uwantaka sun daɗe a tsakani.
Ƙasashen sun bayyana ficewarsu daga ECOWAS ne ba tare da bata lokaci ba, bayna da su ka cimma matsaya a kan hakan kamar yadda shugabannin sojin kasar Nijar su ka bayyana.