Gwamnatin jihar Katsina ta kafa wani kwamiti da zai yi duba dangane da hauhawar kayan masarufi da samar da daidaito a jihar.

 

Mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Jobe ne ya kaddamar da kwamitin mai mutane 27.

 

An kaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis da nufin dakatar da hauhawar kayan masarufi, gano wuraren da aka boye abinci ba bisa ka’ida ba, da kuma daidaita farashin kayan abinci.

 

Kwamitin ya ƙunshi shuwagabannin addinai, shuwagabannin gargajiya, kungiyoyin yan kasuwa da kungiyar direbobi ta ƙasa reshen jihar.

 

Haka kuma za a kula da zirga-zirga da kayan abinci, tare da tabbatar da cewar ba a ƙara farashi ba tare da dalili ba.

 

Hakan na zuwa ne bayan da mutane ke fama da tsadar rayuwa da yunwa, wanda ya sa a wasu jihohin ma aka yi zanga-zanga a kai.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: