Wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun lalata turakun wayar lantarki a jihar Yobe.

 

An lalata turakun guda biyu da ke ƙauyen Kasaisa a kan hanyar Damaturu zuwa Gujiba.

 

A safiyar Juma’a ne su ka yi aika-aikar wanda hakan ya sanya mutane cikin dubu.

 

Wannan shi ne karo na biyu cikin watanni uku, wanda a baya ma makamancin hakan ya jefa jama’a cikin duhu.

 

Jami’an tsaron Operation Lafiya Dole sun tabbatar da haka ta bakin mataimakin jami’in hulda da jama’a Kaftin Shehu Muhammad.

 

Ya ce abin talauci ne yadda su ka lalata turakun.

 

Lamarin da ya sa mutane ke yin kira don ganin an baiwa dukkanin hanyoyin samar da lantarki kariya tare da isasshen tsaro.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: