Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilan da ya sa aka samu tsaiko a rabon kayan hatsin da gwamnatin tarayya za ta raba.

 

Tinubu ya ce za a yi rabon ne wasu daga cikin wurare a ƙasar.

 

Shugaban wanda mai bashi shawara na musamman a kan yaɗa labarai Bayo Onanuga ya yi magana a madadinsa, ya ce ba da jimawa ba za a raba kayan abincin don rage radadi.

 

Ma’aikatar aikin gona a Najeriya ce ta ce za a raba kayan hatsi da su ka kai tan 42,000.

 

Daga cikin kayan hatsin da za a raba akwai masara, da gero da kuma sauran kayan abinci.

 

Onanuga ya ce hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ce ke da alhakin raba kayan abincin, wanda zaa a fara rabawa ba da jimawa ba.

 

Sannan gwamnatin za ta samar da tan 60,000 na shinkafa wanda za ta rabawa ƴan kasar.

 

Ya ce gwamnatin za ta samar da shinkafa daga kamfanonin sarrafa shinkafa don rabawa kuma kyauta.

 

Dukkanin kayan abincin da za aa raba kyauta za a bayar da su.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: