Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na hadin gwiwa da kamfanin Afrinvest (West Africa) Limited domin inganta harkokin kasuwanci da ci gaban jihar.

 

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a bikin bude ofishin Afrinvest na Kano a ranar Alhamis.

 

Gwamnan wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi, Kabiru Sa’id Magami, ya bayyana cewa, babu wani lokaci da ya fi dacewa da Afrinvest ta kafa ofishi a jihar fiye da yanzu.

 

Gwamnan ya taya kungiyar Afrinvest murna kan nasarorin da ta samu a cikin shekaru 30 da suka gabata da kuma zabar Kano a matsayin daya daga cikin wuraren da ta kafa reshe.

 

Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatin jihar za ta baiwa kamfanin duk wani tallafi da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: