Babbar kotu da ke jihar Kano ta dakatar da majalisar jihar kan gyaran fuska a dokokin wasu hukumomi guda uku.

 

Hukumomin uku da ake tababa a kai sun hada da na asusun kula da bangaren shari’a da hukumar fansho da giratuti da kuma hukumar majalisar dokokin jihar.

 

Alkalin kotu, Mai Shari’a, Usman Mallam Na’Abba shi ya yanke wannan hukunci bayan lauyan masu shigar da kara, M. I Umar ya gabatar da korafi.

 

Alkalin ya yi hukuncin ne bayan karbar takardar da shugaba kungiyar ma’aikatan shari’a da sakatarenta su ka yi rantsuwa kan takardar da ke dauke da shafuka 19.

 

Ya ce wannan umarni ya na nufin dakatar da ci gaba da kokarin gyaran fuska kan dokokin da ake magana a kansu.

 

Daga cikin wadanda ake karar akwai Gwamna Abba Kabir Yusuf da kwamishinan shari’a na jihar da kuma majalisar jihar.

 

Sauran sun hada da kakakin majalisar da mataimakinsa da shugaban masu rinjaye da kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar.

 

Idan ba a manta ba, a makon da mu ke ciki wata kotu a jihar Kano ta yi hukunci kan badakalar dala da ake zargin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da aikatawa.

 

Kotun ta yi hukunci inda ta ce hukumar yaki da cin hanci a jihar ba ta da hurumin ci gaba da bincike ko hukunta Ganduje kan badakalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: